Home DUNIYA Buhari: Zan nesanta kai na da Birnin Abuja bayan 2023

Buhari: Zan nesanta kai na da Birnin Abuja bayan 2023

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin nesanta kan sa daga birnin Abuja bayan 29 ga watan Mayu na shekarar 2023, domin kaucewa shugaban da zai gaje shi katsalandan
Shugaban ya bayyana hakan ne lokaci da ya karbi bakuncin mazauna birnin bisa jagorancin ministan birnin Muhammad Bello a fadar shugaban kasa a ranar Lahadi.
A yayin ziyarar gaisuwar bukuwan kirsimeti, shugaban yace zai koma mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya bayan kammala wa’adin shugabancin sa.
Acewar sa kauracewa birnin Abuja shi ne domin bai wa sabon shugaba damar gudanar da aiyukansa ba tare da katsalandan ba.
Haka kuma ya kara da cewa bai gina sabon gida a Daura ko a wani wuri ba, kuma zai koma gidansa domin cigaba da rayuwa bayan cikar wa’adin mulkinsa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp