Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta ce ta samu bayanai da ke nuna cewa wasu ‘yan siyasa na shirin shigo da ‘yan bangar siyasa zuwa jihar domin tayar da hatsaniya a zaɓen gwamnoni da na ‘yan majalisar dokoki da ke tafe.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mamman Dauda shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar, inda ya ce ‘yan siyasa da ke ganin za su fadi, tuni suka shirya tayar da tarzoma a zaɓen da ke tafe a ranar Asabar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sai dai, Mamman Dauda, ya gargaɗi dukkan ‘yan bangar siyasa da wasu ɓata gari cewa kada su kuskura su ta da fitina saboda a shirye ‘yan sanda suke wajen hukunta duk wanda aka kama da laifi.
CP Dauda ya kuma ce rundunar tare da haɗin gwiwar wasu jami’an tsaro a jihar za su tabbatar da cewa an kama dukkan waɗanda ake zargi, inda ya ce duk ɗan bangar siyasa da aka kama, za a tura shi zuwa kotu tare da waɗanda suka saka su aikin.
PRNigeria hausa












