Gwamnan Babban Bankin Najeriya Godwin Emiefele, ya roki afuwar ƴan Najeriya kan matsalar da ake fuskanta wajen tura kuɗi ta intanet. Kwamitin tsare-tsare kan harkar kuɗi
Emefiele ya bayyana haka ne a taron kwamitin tsare-tsare kan harkokin kuɗi da aka gudanar a Abuja, inda ya tabbatar wa ƴan ƙasar cewa za a magance matsalar nan ba da jimawa ba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
A cewarsa, sashin da ke kula da biyan kuɗaɗe na babban bankin, ya yi iya kokarinsa don tabbatar da cewa an magance matsalar, a daidai lokacin da ƴan Najeriya ke ci gaba da fuskantar wahalhalu wajen aika kuɗi da wayoyinsu da kuma a na’urar cirar kuɗi ta POS.
An soma fuskantar matsalar ne tun bayan da gwamnati ta kaddamar da batun sake fasalta kuɗi wanda kuma ya janyo ƙarancin takardun kuɗi a faɗin ƙasar.
“Dole mu bai wa ƴa Najeriya hakuri. Mutane na cikin wahala kan rashin samun aika kuɗi ta intanet. Amma ina ganin ana kokarin shawo kan matsalar,” in ji Emiefiele.
A taron, gwamnan babban bankin ya kuma yi magana kan rashni wadatuwar takardun kuɗi a ƙasar saboda sake fasalin naira, inda ya ce bankin zai ci gaba da buga sabbin takardun kuɗi domin su wadatu musamman ma a kasuwanni.












