Faifen Bidiyon Ganduje na Dollar Gaskiya ne- Muhy

Kwararru masu binciken kwakwaf sun tabbatar da sahihancin faifen bidiyon da ke nuna tsohon gwamnan jihar Kano Dafta Abdullahi Umar Ganduje na cusa daloli a aljihunsa da aka ce cin hanci ne ya karba daga hannun wasu ‘yan kwangila.

Shugaban Hukumar Sauraren Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin hanci ta Jihar Kano Muhyi Magaji Rimin Gado ne ya bayyana hakan a wani taron yini guda kan yaki da cin hanci da rashawa a jihar.

Ta cikin jawabin nasa Muhyi ya ce, an tabbatar da sahihancin faya-fayan bidiyon.

Inda yace tun lokacin da aka saki hotunan bidiyon, jama’a ke ta kalubalantar hukumar da ta wanke gwamnan daga wannan zargi  ko kuma akasin haka.

A shekarar 2017, Jaridar Daily Nigerian da ake wallafawa a yanar gizo ta saki wasu hotunan bidiyon Ganduje na karbar kudadden da ake zargin cewa, na cin hanci ne, al’amarin da ya haddasa cece-kuce a ciki da wajen jihar.

Muhyi ya ce, tun a shekarar 2018 ne suka kaddamar da bincike kan lamarin, amma suka gaza zurfafa binciken Gandujen saboda a lokacin saboda rigar kariya da yake da ita a matsayinsa na gwamna.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1190 days 9 hours 32 minutes 42 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1172 days 11 hours 14 minutes 8 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com