Ana zargin wata mata mai suna Rahimat Salaum da kashe mijinta mai fama da larurar shanyewar ɓarin jiki sannan ta jefar da gawarsa a cikin wani kango.
Lamarin ya faru ne a yankin Pegi da ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Kakakin rundunar ’yan sanda ta shiyyar Abuja, SP Josephine Adeh, ita ce ta tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa da yammacin Talata.
Ta ce tuni jami’an rundunar da ke yankin na Pegi ne suka cafke Rahimat a ranar Litinin.
Read Also:
A cewar Josephine, an kama matar ne lokacin da take ƙoƙarin tserewa da kayayyakin mijin nata, kafin ’yan sanda su yi mata ƙofar-rago su kama ta.
“Bayan an yi mata tambayoyi, wacce ake zargin ta amsa cewa ita ce ta kashe mijin nata bayan wata sa’insa da ta shiga tsakaninsu. Daga nan ne ta yi wa jami’anmu jagora zuwa kangon da ta jefar da gawar tasa, inda aka tarar da shi ya yi mummunar ƙonewa,” in ji Kakakin ’yan sandan.
Sai dai ta ce ’yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin, kuma da zarar sun kammala za su miƙa ta gaban kotu domin ta girbi abin da ta shuka.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 15 hours 20 minutes 56 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 17 hours 2 minutes 21 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com