Home General Jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kashe mutum shida bisa ‘kuskure’ a Katsina

Jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kashe mutum shida bisa ‘kuskure’ a Katsina

Rahotanni daga jihar Katsina na cewa jirgin yaƙin sojin Najeriya ya kashe mutum shida bisa ‘kuskure’ a lokacin da sojojin ke bin wani gungun masu garkuwa da mutane.

Mazauna ƙauyen Zakka a Katsina sun ce jirgin sojin sun jefa bama-bamai a kan rukunun bukkoki, abin da ya janyo sanadiyyar kisan mutum shida.

Luguden wutar kamar yadda wani rahoto ya ce na zuwa ne bayan da wasu ƴanbindiga suka kai wa wani sansanin ƴansanda hari inda suka kashe jami’an guda biyu da ɗan sinitiri guda ɗaya.

Sai dai ƙungiyar Amnestiy International ta nemi da a gudanar da bincike.

Har kawo yanzu sojojin Najeriya ba su ce uffan ba dangane da harin na ‘kuskure’.

A baya dai sun sha bayyana cewa hare-hare irin waɗannan na kuskure ne kuma za a ɗauki matakan kawo ƙarshen afkuwar hakan a gaba.

Wannan ne dai karo na 10 da ake samun irin waɗannan hare-hare na kuskure a shekaru biyu sannan na 11 a tsawon shekaru takwas.

Ko a watan Janairun 2025 ma sai da aka samu irin wannan harin na kuskure a a jihar Zamfara inda fafaren hula 16 suka mutu.

A watan Disamban 2024 ma an samu irin wannan hari a jihar Sokoto wanda ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 10.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp