Home Bincike Bincike: Shin da gaske ne masu zanga-zangar #EndBadGovernance sun kai hari kasuwar...

Bincike: Shin da gaske ne masu zanga-zangar #EndBadGovernance sun kai hari kasuwar hausawa dake jihar Imo?

Akwai wani bidiyo maras kyan gani da ya yake yawo a kafafen sada zumunta na zamani dake ikirarin cewa al’ummar hausawa, da ya hadar da kasuwarsu da ake kira da Avu market aka tarwatsa a yayin zanga-zangar #EndBadGovernance.

Wani bidiyo dauke da wata murya cikin harshen hausa wadda ke ikirarin masu zanga-zanga sun kone dukkan unguwannin da hausawa suke an kone su kurmus a jihar Imo.

Mai Magana na cewa al’ummar hausawa da jagororinsu suka yi watsi da lamurransu, ga halin da suke ciki, ya kuma bukaci dukkan wanda ya kalli bidiyon ya yada domin wani ya gani.

Domin tabbatar da sahihancin ikirarin PRNigeria ta bincike bidiyon a nutse, inda ta karkasa shi kashi-kashi, domin yin amfani da hanyar gano ingancin bidiyo na (reverse image search)

Sakamakon ya nuna man cewa an wallafa bidiyon a shafin facebook mai suna Nuru Shehu, shekara daya da ta gabata, a ranar 29 ga watan yunin 2023.

Wallafar a shafin facebook ta sami like dubu 9, inda mutane dubu 1 da dari 7 suka tofa albakacin bakinsu, mutane dubu 13 suka sake yada shi, sai mutane dubu dari 433 suka kalla.

A cigaba da bincike,  PRNigeria ta kira kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Imo ASP Okoye Henry, wanda ya tabbatar da cewa babu wata zanga-zanga da aka gudanar wadda ta kai ga tarwatsa kasuwancin hausawa.

ASP Okoye ya kara tabbatar da cewa bidiyon dake yawo aiki ne kawai na marasa son zaman lafiya, wanda kullum bukatarsu shi ne yadda wani bangarorin kasar zasu kasance cikin tashin hankali da juna.

Ya bayyana cewa bidiyon dake yawo na wata gobarace da ta kama a kasuwar ta Avu, a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

KAMMALAWA: bisa binciken da PRNigeria ta gudanar ikirarin cewa an kone wurin zaman ‘yan Arewa da kasuwarsu a jihar Imo a lokacin zanga-zanga ba gaskiya bane labara ne na raba kawunan Al’umma.

By PRNigeria

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp