Home Taska NITDA ta ba wa F.U.D Gudumawar Na’ura Mai Ƙwakwalwa Guda 150

NITDA ta ba wa F.U.D Gudumawar Na’ura Mai Ƙwakwalwa Guda 150

NITDA ta ba wa F.U.D Gudumawar Na’ura Mai Ƙwakwalwa Guda 150

Hukumar bunƙasa fasahar sadarwar zamani ta ƙasa, (NITDA), ƙarƙashin jagorancin Malam Kashif Inuwa Abdullahi, (CCIE), bisa kulawar ma’aikatar sadarwa da tattalin arziƙin zamani, ƙarƙashin jagorancin Farfesa Isah Ali Ibrahim Pantami, (FNCS, FBCS, FIIM), a wannan rana ta ba da gudunmawar na’ura mai ƙwaƙwalwa (Computers) jimillar guda (150) ga jami’ar gwamnatin tarayya da ke birnin Dutsen Jihar Jigawa, “Federal University Dutse”, (F.U.D).

A rahoton da jami’ar ta fitar ta cikin shafinta na sadarwa na (Facebook), sun bayyana cewa: daga cikin jimillar kwamfiyutocin, guda (100) waɗanda ake ɗorawa ne akan tebur, (Desktop Computers), samfurin kamfanin (Lenovo), sai kuma guda (50) na tafi da gidanka, (Laptops), samfurin ƙirar babban kamfanin nan na (HP).

Da ya ke jawabi a lokacin da ya ke gabatar da gudunmawar ga hukumar jami’ar, mai girma shugaban na (NITDA), Malam Kashif Inuwa, wanda Hannah Peter ya wakilta, ya bayyana cewa dalilin ba da gudunmawar shi ne domin a bunƙasa koyo da koyarwa na zamani a jami’ar.

A nasa martanin a ya yin da ya ke karɓan gudunmawar, muƙaddashin shugaban jami’ar, (VC), Farfesa Abdulkarim Sabo Muhammad, wanda shugaban tsangayar fasaha da kimiyyar zamantakewa, Farfesa Lawan Shu’aibu, ya wakilta, ya godewa shugaban na (NITDA), bisa wannan gagarumar gudunmawa wacce ya ce za ta taimaka wajen bunƙasa sha’anin koyo da koyarwa ta hanyar fasahar sadarwar zamani, tare kuma da cika babban burin shugaban jami’ar na ɗora ta akan turbar fasahar zamani.

Ƙarawa da cewa: “Shugaban (NITDA) mutum ne mai salo daban-daban, sannan mutum ne sahun farko wanda ya himmatu ka’in da na’in wajen samar da nagartattun ayyukan fasahar zamani a jami’o’in Nageriya domin ganin sun dace da (ƙarni na 21). Jami’armu ta (FUD) ta yi haɗin gwiwa akan abubuwa da dama tare da (NITDA), musamman a fannin harkar noma a ƙarƙashin cibiyarmu ta nazari da bincike kan noma, jami’armu ta na godiya ta musamman ga shugaban na (NITDA) akan wannan al’amari. Cewar shugaban (FUD), Farfesa Muhammad.

Lahadi, 20 ga watan Fabarairu, 2022.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Amurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba Hatsarin Jirgin Sama na Ondo: Disu Ya Jajantawa NAF, Ya Jaddada Goyon Bayan Ƴan SandaHukumar Kwastam ta Kwace Wiwi ta N3.67bn da Aka Boye a Cikin Motocin da Aka Shigo da su, da Sauran Kayayyaki a Tashar Jirgin Ruwa ta LegasFadada Rundunar Soja: COAS ya Yabawa Gwamnatin Nasarawa Kan Karbar Sabbin SojojiTaron Talla na Ƙasa 2026: Farfesa Sule Ya'u Sule zai yi Magana Kan Harshe, Al'adu da Talla a Arewacin NajeriyaSojoji Sun Yaye Kwamandoji na Musamman Domin Yaki da Ta'addanci da Jiragen Yaki Marasa MatukaMinista Ya Yaba da Aikin Babban Titin Tarayya na N1.5trn a Jihar Neja
X whatsapp