Home Taska ‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Sarkin Pushit da ke Jahar Filato

‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Sarkin Pushit da ke Jahar Filato

‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Sarkin Pushit da ke Jahar Filato

Mutanen kauyen Pushit sun ga ta kansu yayin da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da Mai garinsu.

A ranar Alhamsis aka ji ‘yan bindiga sun shigo Pushit, sun yi awon-gaba da Diket Gupiya a gidansa.

Jami’an ‘Yan Sanda da wasu mazauna wannan gari sun tabbatar da sace Mai martaba Diket Gupiya.

Plateau – Hankalin Bayin Allah ya tashi a karamar hukumar Mangu da ke jihar Filato bayan sace wani Basarake. Jaridar Punch ta fitar da wannan rahoto a yau.

Kamar yadda muka samu labari, ‘yan bindiga sun sace Mai martaba Diket Gupiya a Mangu.

Mai martaba Diket Gupiya shi ne mai rike da kasar Pushit. Daga wannan yanki a garin Mangu ne mataimakin gwamnan jihar Filato watau Sonny Tyoden ya fito.

Ana zargin wadannan ‘yan bindiga sun dauke Sarkin Pushit a fadarsa da ke kauyen Pushit a cikin daren ranar Alhamis din ta wuce, 24 ga watan Fubrairu 2022.

Wata majiya da shaidawa jaridar ta Punch cewa Diket Gupiya yana cikin gidansa yana kallon talabijin da kimanin karfe 9:00 na dare ne aka shigo masa daki.

Wadannan miyagu sun kawo hari, suka kuma yi nasarar yin awon gaba da Basaraken a jiya.
‘Yan bindigan sun yi gaba da Gupiya.Kawo yanzu ba a samu wani labari a game da inda aka kai shi ba. Ana tunanin za a nemi a biya kudin fansa kafin ya fito

. Tuni dai jami’an ‘yan sanda na jihar Filato ta bakin Ubah Ogaba sun bayyana cewa sun san da aukuwa lamarin, kuma an tura dakaru domin su ceto Gupiya.

Mun shiga uku – ‘Yan gari

Wani mazaunin yankin, Philip Moses ya shaidawa ‘yan jarida cewa an dauke Sarkin da ya taba neman canza sunan garinsa. Newsngr ta fitar da wannan rahoto.

“Abin takaici ya sake auka mana, an yi garkuwa da Cif Diket Gupiya, Mai garin mu a kasar Pushit a jiya Alhamis cikin dare.” – Philip Moses.

An kuma dauke Sarki

Ba wannan ne karon farko da aka ji irin wannan labari ba. Watanni biyu da suka wuce an ji cewa ‘yan bindiga sun sace Sarkin kasar Gundiri, Charles Mato.

Mai martaba Sum Pyem na Gundiri watau Charles Mato bai fito ba sai da aka biya kudin fansa. Wani ‘danuwan Sarkin ya bada labarin abin da ya wakana.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp