Home Labarai ‘Yan Sanda a Jihar Zamfara Sun Sami Nasarar Kubutar da Mutane 39...

‘Yan Sanda a Jihar Zamfara Sun Sami Nasarar Kubutar da Mutane 39 da Hannun ‘Yan Bindiga

Rundunar ‘Yan Sandan Nijeriya ta sami nasarar kubutar da mutum 39 Mafi yawan su mata da kananan Yara da ‘Yan Bindiga sukayi garkuwa dasu a  jihar Zamfara.

Kakakin hukumar ‘Yan Sandan Jihar ta Zamfara Muhammad Shehu, ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa, inda yace wadanda aka kubutar din na cikin wadanda ‘Yan bindigar sukayi garkuwa dasu a kauyukan dake kananan hukumomin Maru da Bungudu.

“Wadanda aka kubutar sun hadarda Maza 8 Mata 15 cikin su harda masu shayarwa da kuma kananan yara 16” a cewar sa.

“Nasarar ta biyo bayan wani aikin share fage da Rundunar ‘Yan Sanda hadin Gwuiwa da Rundunar Soji suka gudanar a sansanin Dabar Magaji dake dajin Kadanya wanda ke tsakanin Kananan Hukumomin Kaura Namoda da Maradun.

Ya kara da cewa, “ ‘Yan sanda da hadin gwuiwar kungiyar likitocin Gwamnatin Jihar sun dukufa domin bawa wadanda aka ceto kulawa ta musamman, inda daga bisani kuma za’a mika su ga iyalan su, a cewar sa.

Rundunar ‘Yan Sandan ta ce ta sami nasarar kame wasu mutum 10 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban daga cikin su akwai ‘yan haramtacciyar kungiyar ‘yan Sakai.

Yan Sakai kungiya ce ta ‘Yan banga da ke aiki a cikin yankin Arewa Maso Yamma, yawancin su mafarauta ne da ke aiki da Jami’an tsaro don kare Al’ummarsu daga ‘Yan fashin da ke kai farmaki a kauyuka da gonaki.

Daga cikin mutane goman da rundunar ta sami nasarar kamawa akwai mutum 3 da ake zargi da yin garkuwa da mutane 2 a unguwar fakon Idi dake talata mafarada kuma wasu mutane 2 da aka kama da laifin shiga gidaje da satar wayoyin hannu a Gusau babban birnin jihar ta Zamfara.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp