Home Labarai Zamu ɗaukaka ƙara kan wanke Oronsaye daga zargin cin hanci – EFCC

Zamu ɗaukaka ƙara kan wanke Oronsaye daga zargin cin hanci – EFCC

Hukumar da ke yaƙi da masu yi wa tattali arzikin Najeriya zagon ƙasar EFCC ta ce za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin da wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta yanke, na wanke tsohon shugaban ma’aikata na ƙasa daga zargin halasta kuɗin haram da suka tasamman naira biliyan biyu da hukumar ke yi masa shi da wasu.

A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce za ta ƙalubalancin hukuncin a gaban kotun ɗaukaka ƙara.

Hukumar dai na zargin Steve Oronsaye da mutunen da ake zarginsu tare da yin amfani da wasu kamfanoni wajen karkatar da kuɗin gwamnati ta hanyar amfani da kwangilolin bogi.

Yayin da yake watsi da ƙarar, alƙalin kotun mai shari’a Inyang Ekwo ya ce hukumar EFCCn ta kasa tabbatar da zarge-zargen da take yi wa mista Oronsaye.

To sai dai a cikin sanarwar da mai magana da yawun hukumar Wilson Uwujaren ya fitar ya ce alƙalin ya yi kuskure, saboda a cewarsa bai yi la’akari da shaidun da masu ƙara suka gabatar ba, a tsawon shari’ar, tare da bahasin da ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙarar Osarenkhoe Afe ya furta da bakinsa a gaban kotun.

A shekarar 2015 ne hukumar EFFC ta gurfanar da Mista Oronsaye tare da shugaban kamfanin Fredrick Hamilton Global Services Limited, Osarenkhoe Afe da wasu kamfanoni uku bisa zarginsu da yin amfani da wasu kamfanoni wajen karkatar da kuɗin gwamnati ta hanyar amfani da kwangilolin bogi.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mutane 200 Sun Mutu Sakomakon Girgizar ƙasar a ColombiaShahararren Mawaƙin Najeriya, Davido ya Rubuta wa Trump Wasiƙa Kan Zaɓen Jihar OsunHukumar NHRC ta Buƙaci a Kama Malamin Addinin, Sheikh JingirRundunar sojin Najeriya ta Daƙile Shirin Ƴan Bindiga a FilatoJami'an Ƴan Sanda 10 Sun Mutu Yayin Artabu da Ƴan Bindiga a Jihar KebbiAn Naɗa ɗan Najeriya Gidado Shuaib Wakilin Matasa na IPRA-UN Gabanin GWAEFCC da "Wuce Gona da Iri" da Tambayar 2027: Shin ana Rudar da Tinubu ta Hanyar Mutanen da ke Kewaye da Shi ? Daga Yushau A. ShuaibAn Samu Gawar Yara 3 da guda 1 a Sume a Gidan Mai Maganin GargajiyaMene ne Ainihin Abin da ya faru Aka Rufe Asusun Bankunan Gwamnatin Osun ?Jami'an Tsaro Sun Ceto Mutane 308 a Jihohin Arewacin Najeriya An Kama Mutane 6 da Ake Zargin da Taimaka wa Mayaƙan ISWAP a Jihar BornoZaɓen 2027: PDP ta Miƙa Sunan Jonathan ga INEC a Matsayin ɗan Takararta na Shugaban ƙasaIyanen Babban Jami'in Kula da Harkokin Kuɗaɗen ƙungiyar ISWAP Sun Miƙa Wuya ga SojojiAna Zargin Mayaƙan Boko Haram da Kashe Sojojin Nijar 14Gombe 2027: Malamai da Mambobin APC Sun yi Allah-wadai da Sukar Rarara ga Pantami
X whatsapp