Home Labarai Majalisar Dattijai Ta Tabbatar da Farfesa Abdullahi Saleh A Matsayin Shugaban Hukumar...

Majalisar Dattijai Ta Tabbatar da Farfesa Abdullahi Saleh A Matsayin Shugaban Hukumar NAHCON

Majalisar kasa ta tabbatar da nadin Farfesa Saleh Abdullahi Usman a matsayin sabon shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON).

ya karbi mukamin shugaban hukuma na 6 bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da tsohon shugabanta Malam Jalal Ahmed Arabi daga shugancin hukumar.

A sanarwar da Mataimakiyar Daraktar harkokin hulda da Jama’a ta Hukumar, Fatima Sanda Usara ta sanyawa hannu, tace, tabbatar da hakan na zuwa ne bayan kwamitin majalisar dattawa kan harkokin kasashen waje ya tantance Farfesa Usman a ranar 8 ga Oktoba 2024.

Tabbatar da hakan ya nuna amincewar Majalisar ga sabon Shugaban Hukumar NAHCON ta hanyar gudanar da ayyukanta na tabbatar da aikin Hajji mai inganci da nasara ga Alhazan Najeriya.

Farfesa Sale Abdullahi ya nuna jin dadinsa kan amanar da bangarorin gwamnati da na majalisar dokoki suka ba shi.

Ya yi alkawarin dorawa kan nasarorin da Shugabanmin da suka gabace shi suka samu wajen tabbatar da ci gaban aikin Hajji a Najeriya, tare da mai da hankali kan jin dadin alhazan Najeriya da yadda za su iya gudanar da aikin Hajji mabrur (Hajji karbabbe).

Bayan Da majalissar dokokin kasar ta tabbatar da Farfesa Usman, ya ba da tabbacin ci gaba da jajircewa wajen ganin hukumar NAHCON ta bunkasa da kuma neman addu’a da goyon bayan kowa wajen cimma burin masu ruwa da tsaki.

“Za mu ci gaba da inganta ayyukanmu ga mahajjatan Najeriya, tare da yin aiki kafada da kafada da duk masu ruwa da tsaki don samar da aikin hajji mai cike da aminci.”

Shugaban ya taba yin aikin a karkashin Hukumar Jin Dadin Alhazai ta Jihar Kano a matsayin Shugaban Hukumar.

Canjin shugabancin ya zo ne a daidai lokacin da hukumar NAHCON ke shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana a daidai lokacin da Saudiyya ta kayyade.

Ana sa ran tabbatar da Shugabancin zai hanzarta shirye-shiryen. Ana kuma sa ran za a kara inganta hadin gwiwar Hukumar da duk masu ruwa da tsaki domin tabbatar da nasarar aikin Hajji ga dukkan maniyyatan Najeriya.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Darakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da Wiwi
X whatsapp