Rundunar sojin Najeriya ta ce bama-baman da Lakurawa suka ajiye a ƙauyukan da sojojin suka kai wa hari ne suka kashe mutanen gari, ba hare-haren da sojojin suka ƙaddamar ba.
Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron Najeriyar ta fitar mai ɗauke da sa hannun daraktan yaɗa labaranta, Manjo Janar Edwar Buba ta ce ba harin sojojin ne ya kashe mutanen ba.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Jami’in ya ce kafin kai harin, sai da sojojin suka ɗauki tsawon lokaci suna gudanar da bincike ta hanyar tattara bayanan sirri, kuma sai da suka tabbatar da cewa Lakurawa ne ke kai kawo a yankin kafin afka musu.
A ranar Laraba ne aka samu rahotonnin hare-haren jiragen sojin Najeriya a wasu ƙauyuka biyu da ke yankin ƙaramar hukumar Silame a jihar Sokoto.
Gwamnan jihar, Ahmad Aliyu ya ce sojojin ƙasar ne suka kai harin bisa kuskure, lamarin ya yi sanadin mutuwar mutune 10.











