Gwamnatin jihar Zamfara ta amince da naira 70,000 a matsayin sabon albashi mafi ƙanƙanta.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ya ce daga yanzu ma’aikatan jihar za a fara biyan ma’aikatan jihar da sabon tsarin albashin.
Ya kuma ce gwamna Dauda Lawal ya amince da ƙarin albashi ko kuma alawus na ƙarin wata ɗaya ga ma’aikata a faɗin jihar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
“Wannan shi ne irinsa na farko a tarihin Zamfara, wanda kuma gwamna Dauda Lawal ya biya a cikin watan Disamba,” in ji sanarwar.
Kakakin gwamnan ya ce dukkan ma’aikatan jihar, ciki har da waɗanda suka yi ritaya za su samu kashi 30 na alawus.
Gwamnan Dauda Lawal ya ce ya amince da albashi mafi ƙanƙantan da kuma alawus ne domin taimakawa ma’aikatan jihar a wannan lokaci na bukukuwan karshen shekara da kuma ƙara musu karfin gwiwa wajen aiki tukuru wajen kai jihar gaba.











