KORAFI: Akwai wani rubutu dake yawo a kafafen sada zumunta na zamani (Facebook) cewa a jihar Ekiti an yi tikitin Kirista – Kirista daga shekarar 2010 – 2018.
CIKAKKEN BAYANI: A cikin wani shafin facebook; mai Suna Buharist Reporter, an wallafa wani rubutu a ranar 30 ga watan Yuni, wanda ke kunshe da jerin jadawalin ‘yan siyasar da suka gabata wadanda suka taba yin takarar shugabancin Nijeriya ko kuma gwamna a wata jihar da suka dauki mataimakin su daga cikin mabiya Addini Kirista, rubutun da aka yiwa lakabi da “FLASHBACK CHRISTIAN-CHRISTIAN TICKET” ya Ambato sunan Mista Ayo Fayose wanda ya Mulki jihar Ekiti daga shekarar 2014 zuwa 2018 tare da mataimakin sa, Niyi Adebayo, tikitin Kirista-kirista ne amma Al’ummar Musulmi basu ce komai kan lamarin ba.
Haka kuma shafin ya mabato sunan Gwamna Kayode Fayemi na Ekiti tsakanin shekara 2010 zuwa 2014 ya dauki kirista a matsayin mataimaki sa.
BINCIKEN TABBATARWA: PRNigeria ta gudanar da wani bincike da ya tabbatar mata da cewa Dr. Kayode Fayemi da Mr Ayo Fayose sun gudanar da tikitin kirista – kirista a yayin da suke takarar zaman gwamnan jihar kuma bayan gudanar da zaben sun sami nasarar.
Read Also:
A tsakanin shekarar 2010 zuwa 2014, Dr Kayode Fayemi ya dauki Kirista a matsayin wanda zai masa mataimaki, Funmilayo Olayinka karkashin Inuwar jam’iyyar (ACN), wanda daga bisani ya mutu a ranar 6 ga watan Afrilun 2013.
Ta cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 3 ga watan Mayu, shekarar 2013, yayin da yake jawabi ga kakakin majalisar dokokin jihar Adewale Omiri, ya bukaci majalisar ta aminci da nadin farfesa Modupe Adelabu, wanda shima mabiyin addinin kirista ne, matsayin mataimakin Gwamnan jihar, domin cike gurbin mataimakin gwamnan jihar da ya mutu.
Haka kuma Ayo Fayose ya gudanar da tikitin kirista-kirista tsakanin shekarar 2014 zuwa 2018 a karkashin inuwar jam’iyyar “People Democratic Party” PDP. Inda ya dauki Farfesa Kolapo Olusola Eleka, wanda shima mabiyin addinin kiristanci ne.
KAMMALAWA: Sakamakon bayanan da PRNigeria ta tattara a jihar ya tabbatar mata da cewa Mista Ayo Fayose da Dr. Kayode Fayemi sun gudanar da tikitin Kirista-kirista a mabambanta lokaci a jihar ta Ekiti.
By PRNigeria
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 54 minutes 49 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 36 minutes 14 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com