Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara tace mutum bakwai 7 ‘yan gida daya ne suka mutu sakamakon cin dambu a matsayin abinci dare a jihar
Kakakin rundunar SP Mohammad shehu ne ya bayyana hakan ga manema labarai, cewa rundunar na kan bincike kan lamarin, domin gano musabbabin mutuwar mutane ‘yan kauyen Danbaza dake karamar hukumar Maradun.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
“lamarin ya auku ne ranar litinin bayan iyalan sun ci wani abinci da suka girka a matsyain abinci dare.
“Mun dauki samfurin abincin da suka ci, kuma ana kan bincike, da zarar an kamala kuma zamu sanar da manema labarai,” a cewar Muhammad Shehu.
Wani mazaunin kauyen muhamma Kabir kuma makusance ga mamatan ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya cewa hudu cikin wadanda suka mutun 2 matan aure ne sun mutu nan take, yayin da 5 kuma sai da aka garzaya da su asibiti, kafin suka ce ga garin ku nan.












