Home DUNIYA Ambaliyar Ruwa ta Hallaka mutane 9 a Afirka ta Kudu

Ambaliyar Ruwa ta Hallaka mutane 9 a Afirka ta Kudu

Mutum tara sun mutu yayin da takwas suka ɓace sakamakon ambaliyar da wani kogi ya yi, inda ya tafi da masu bauta a wani coci.

Shaidu sun ce fiye da masu bauta 30 ne ke tsaye a kan duwatsun da ke kusa da kogin lokacin da ruwan mai gudun gaske ya ratso ta inda suke.

Shaidar ta ƙara da cewa an tsamo Faston da ke jagorantar ibadar bayan da ya maƙale cikin tarin bishiyoyin da ruwan ya taho da su.

Masu aikin ceto da suka haɗar da ‘yan sanda da jami’an kiyaye aukuwar bala’i na ci gaba da nemo waɗanda ruwan ya tafi da su.

Robert Mulaudzi mai magana da yawun ma’aikatar bayar da agajin gaggawa ta ƙasar ya ce sun samu gawa biyu ranar Asabar, tare da ceto mtum ɗaya wanda ya ce an kai shi asibiti domin kula da lafiyarsa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp