Mazauna wasu kauyuka da ke karamar hukumar Bakori a Jihar Katsina na zaman makoki sakamakon rasa yan uwansu da dama.
Hakan na zuwa ne yayin da wasu yan ta’adda suka kashe a kalla Yansakai 41 tare da raunata 2 yayin wani artabu a dajin Yargoje.
Rundunar yan sandan jihar Katsina ta tabbatar da afkuwar lamarin tana mai cewa Yansakai din sun bi yan ta’addan daji ne da nufin kwato shanu da suka sace.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Jihar Katsina – Wani artabu da aka yi tsakanin yan ta’adda da kungiyar tsaro ta yan sa kai da aka haramta ayyukansu ya yi sanadin mutuwar a kalla mutum 41 a Katsina.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin ta cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a.
Yansakai sun bi sahun yan bindigan ne bayan sun sace shanu Ya ce yan haramtaciyyar kungiyar ta Yansakai daga kauyuka 11 a karamar hukumar Bakori, sun hadu sun bi sahun yan ta’addan da nufin karbo shanu da suka sace.
Mai magana da yawun yan sandan ya ce mambobin haramtaciyar kungiyar sun bi sahun yan ta’addan sun gano su a wani wuri a dajin Yargoje inda yan ta’addan suka musu harin kwaton bauna.












