Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ya taya zaɓaɓɓen gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar 18 ga watan Maris.
Cikin wata wasiƙa da ya aike da ita, Sarkin Kano ya ce ya fahimci mutane sun karɓi dimukradiyya hannu biyu-biyu, kuma abu mafi mahimmaci shi ne yadda suka fito suka kaɗa kuri’unsu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Gabanin haka shi ma Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Ibrahim Gaya ya aike da ta shi wasiƙar taya murna ga sabon zaɓaɓɓen gwamnan, wanda ya ce a madadinsa da iyalansa ya aika sakon.
Sarkin Rano ma Alhaji Kabiru Muhammad Inuwa ya aike da na shi saƙon tare da fatan Allah ya taya sabon shugaban riƙo da shugabancin mutanen Kano.
Duka sarakunan sun miƙa godiya ga malaman addinai da shugabannin jama’a da suka riƙa wayar da kan al’umma, aka yi zaɓe lafiya aka gama lafiya.












