Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya ce babban aiki mafi muhimmanci da ke gaban Musulman duniya a yau shi ne yada akidu da ilimin addinin Musulunci na gaskiya.
Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a birnin Madina na kasar Saudiyya, a ziyarar aikin Umara da yake yi.
Read Also:
A cikin wata sanarwa da aka fitar mai dauke da sa hannun Malam Garba Shehu, mai bai wa shugaban shawara kan kafafen yada labarai, Buhari ya kuma yaba wa gwamnatin Saudiyyar bisa yadda ta samar da kayayyakin zamani wajen yada Musulunci da sanin manufarsa a ilmance kuma ta hanya mafi inganci.
Da yake bayani bayan rangadi a wajen baje-kolin kasa da kasa da kuma zagaya gidan adana kayan tarihin fiyayyen halitta Annabi Muhammad SWA da Sakafar Musulunci a wani bangare na ayyukan da yake yi a Saudiyya, Shugaban Nijeriyar ya ce al’ummar Musulmai na bukatar tsari ingantacce da zai bayar da hikima da ilimi domin kyakkyawar fahimtar addinin.
Buhari Ya yaba wa mahukuntan Saudiyya bisa yadda suka yi kokarin yada sakafar Musulunci a duniya, amma kuma ana bukatar karin ayyuka da dama.
PRNigeria hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 18 hours 23 minutes 14 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 4 minutes 39 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com