Masu gadin tekun Tunisia sun ce sun gano gawarwakin ‘yan cirani 41 a cikin tekun.
Wani babban jami’i ya ce sama da ‘yan cirani 200 ne da ke son tsallakawa Turai suka nutse a ruwan cikin kwanaki 10 da suka gabata.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ƙara da cewa mutuwaren ƙasar Tunisia ya cika maƙil da gawarwakin ‘yan cirani amma hukumomin ƙasar na ƙoƙarin shawo kan tururuwa masu yunƙurin tsallakawa.
Ƙasar da ke arewacin Afrika yanzu ta maye gurbin makwabciyarta Libya a matsayin babbar hanyar tsallakawa Turai ga masu cirani.











