Darajar Naira ta fadi kasa a Nijeriya

Darajar naira ta ƙara yin ƙasa a kasuwar canji da gwamnati ke amfani da ita ta Investors and Exporters (I&E) a ranar Juma’a, yayin da Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya dakatar da Gwamnan Babban Banki Godwin Emefiele.

Jaridar Punch a Najeriyar ta ruwaito cewa kasuwar ta tashi a ranar Juma’a ana canzar da dala ɗaya kan naira 471.32.

Rahoton ya ƙara da cewa da farko nairar ta ɗan ragu da kwabo 64, idan aka kwatanta da darajarta ta 469.50 a ranar Alhamis. Sai dai kuma ta ƙara faɗuwa har zuwa 471.32 kan dala ɗaya.

Bola Tinubu ya dakatar da gwamnan bankin ne nan take cikin wata sanarwa, inda aka umarce shi da ya miƙa ragamar CBN ɗin ga mataimakin gwamna mai kula da harkokin gudanarwa, Folashodun Adebisi.

Mista Adebisi zai kasance muƙaddashin gwamna har sai an kammala binciken zarge-zarge a kan Emefiele da kuma sauye-sauye a bangaren kuɗi, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

PRNigeria hausa

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1239 days 14 hours 41 minutes 42 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1221 days 16 hours 23 minutes 7 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com