Matar shugaban Nijeriya Uwargida Oluremi Tinubu ta karbi Rebecca Kabu guda cikin daliban Makarantar Chibok 277 da mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2014.
Oluremi ta karbi dalibar ne a fadar shugaban kasa dake Villa tare da matar mataimakin shugaban kasar , Hajia Nana Shettima, inda tayi alkawarin lura da lafiya ta tare da daukar nauyin karatunta.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ta kuma tabbatar da cewa ba a manta da sauran daliban da ke tsare a hannun ‘yan ta’addan ba.
Haka Kuma ta yaba da kokarin ofishin babban mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da sauran jami’an tsaro bisa kokarin su na kubutar da Rebbeca.
An dai sace daliban na makarantar Chibok ne a wani hari da mayakan kungiyar Boko Haram suka kai kan daliban Makarantar ta Chibok dake Jihar Borno a Arewa maso ga bashin Nijeriya tun a shekarar 2014.
PRNigeria hausa












