Home DUNIYA Burkina Faso za ta aika wa Nijar kayan abinci

Burkina Faso za ta aika wa Nijar kayan abinci

Wasu rahotanni na bayyana cewa Gwamnatin Burkina Faso na shirin aika wa da maƙwabciyarta Nijar hatsi.

Wata sanarwa da ma’aikatar cigaban kasuwanci ta ƙasar ta fitar ranar Juma’a ta ce za a aika wa Nijar ɗin gero da masara da dawa, da dai sauransu.

Yunƙurin na zuwa ne yayin da ƙungiyar ECOWAS  ta ƙaƙaba wa Nijar takunkuman kasuwanci da na tattalin arziki sakamakon juyin mulkin da ya kifar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum a ƙarshen watan Yuli.

Duk da cewa Burkina Faso mamba ce a ECOWAS, ba ta bi umarnin ƙungiyar ba ta raya tattalin arziƙin Afirka ta Yamma saboda ita ma tana cikin takunkumai na juyin mulki.

Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan kasuwar da ke da sha’awar safarar kayan su tuntuɓi hukumomin da suka dace don isar da kayan zuwa Nijar.

Burkina Faso, da Mali, da Guinea dukkansu mambobin Ecowas da aka dakatar saboda juyin mulki, sun sanar da cewa za su goya wa sojojin mulkin Nijar baya idan ƙungiyar ko kuma dakarun ƙasar waje suka kai musu hari.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp