NLC da TUC sun magantu kan rufe filin jigin saman Abuja

kungiyoyin Nijeriya da suka shirya gudanar da zanga-zangar da ta haifar da rufe filin jirgin saman Abuja sun magantu.

tun dai da safiyar Alhamis ne aka hangi yadda motoci da masu ababen hawa suka tsaya jingum-jingum a kan titin.  ana iya ganin wata motar dakon kaya daga nesa an gindaya ta a tsakiyar titi.

Haka zalika, an jiyo kade-kade na tashi, yayin da ake iya hango wasu mutane sanye da tufafi iri daya a kan motocin da ke nesa.

Sakataren tsare-tsare na kungiyar NLC, Kwamared Nasir Kabir ya shaidawa manema labarai cewa mambobinsu sun rufe titin shiga filin jirgin saman na Abuja da kuma hana duk wani jirgin sama da ke da niyyar tashi zuwa jihar Imo.

Haka kuma wata sanarwa da babban sakataren NLC, Kwamared Emmanuel Ugboaja ya fitar ta ce matakin ya hadar da filin jirgin sama na Lagos.

Ta kuma ambaci matakin da ‘yan kwadagon ke dauka a dambarwarsu da gwamnatin jihar Imo.

A ranar Laraba dai 8 ga watan Nuwamban 2023, kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka fara wani yajin aiki, wanda suka sanar da rufe duk wasu harkokin samar da lantarki da na sufurin jiragen sama a jihar ta Imo.

Matakin na zuwa ne kwanaki kalilan bayan zargin da kungiyar NLC ta yi wa gwamnan jihar Hope Uzodinma da hadin bakin ‘yan sanda wajen kama shi tare da dukan sa. ‘Yan kwadagon daga bisani sun nuna hoton shugaban kungiyar NLC, Joe Ajaero da idonsa na dama a kumbure.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 19 hours 28 minutes 16 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 9 minutes 41 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com