Ƴan bindiga sun kai hari kan wani masallaci a karamar hukumar Birnin Gwari ta jihar Kaduna, tare da kashe wasu masallata guda biyu.
Hukumomin ƴansanda a jihar sun tabbatar da afkuwar lamarin.
Wani shugaban al’umma a karamar hukumar, ya shaida wa gidan talabijin na Channels cewa ƴan bindigar sun afka wa masallacin ne a anguwar Makera da ke yankin Kwasakwasa da misalin karfe 2 ranar Juma’a, inda suka buɗe wuta kan masallatan.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Ya ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutum biyu.
A cewarsa, ƴan bindigar sun isa masallacin ne lokacin masu salla ke kai raka’a ta biyu, inda wasu daga cikin suka tsere.
Harin na ranar Juma’a na zuwa ne kwana guda bayan da ƴan bindiga suka sace ɗalibai 287 a wata makarantar sakandare a Kuriga da ke karamar hukumar Chikun na jihar ta Kaduna.
PRNigeria Hausa












