Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta gabatar da buƙatar ƙarin sabon albashi mafi karanci na N615,000 domin magance kalubalen tattalin arziki da tsadar rayuwa da ma’aikata ke fuskanta a kasar.
Shugaban kungiyar ne ya tabbatar da hakan a yayin wata ganawa da gidan talabijin na Channels a ranar Lahadi.
An cimma sabon albashin N615,000 duk wata bayan tattaunawa tsakanin ƙungiyar kwadago ta NLC da TUC ne da nufin rage matsalolin kudi da ma’aikatan Najeriya ke fuskanta.
Kungiyoyin kwadagon sun ce mafi karancin albashi na N30,000 a halin yanzu ba zai iya biyan buƙatun talakawan Najeriya ba, suna masu korafin cewa ba dukkan gwamnoni ne ke biyan albashin ma’aikata na yanzu ba wanda zai ƙare a watan Afrilu, shekaru biyar bayan tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan dokar mafi karancin albashi ba 2019 inda za a sake duba dokar duk bayan shekaru biyar.
Kungiyoyin NLC da TUC a lokuta daban-daban sun yi kira ga gwamnatin shugaba Bola Tinubu da ta gaggauta sake duba mafi ƙarancin albashin ma’aikata.
Read Also:
A farkon watan Janairu ne gwamnatin tarayya ta ƙaddamar da wani kwamitin mutum 37 kan mafi karancin albashin ma’aikata na kasa.
Da farko dai ƙungiyar kwadago ta NLC ta sanar da naira miliyan ɗaya a matsayin sabon mafi karancin albashi, sakamakon hauhawar farashin kayayyaki a kasar da ya jefa mutane da dama cikin talauci.
Yayin da kuma TUC ta buƙaci naira 447,000 a matsayin sabon mafi karancin albashi na wata-wata ga kowane ma’aikaci, wanda daga baya kuma NLC ta bukaci N794,000 ga kowane ma’aikaci.
Amma ƙungiyoyin biyu, a wata sabuwar shawara ga gwamnati, sun buƙaci naira 615,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata.
Kungiyoyin sun ce hauhawar farashin kayayyaki – wanda ya kai kashi 31.70 cikin 100 a watan Fabrairun 2024 ya shafi tsadar rayuwa ga matsakaitan ma’aikatan Najeriya.
Sun kuma lura da cewa gwamnonin jihohi za su iya biyan kowane ma’aikacin gwamnati albashi saboda a yanzu suna samun karin kudaden shiga kowane wata daga hukumar dake tattara da raba arziƙin ƙasa (RMAFC).
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 27 minutes 7 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 8 minutes 32 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com