Hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ta ce hauhawar farashi ta kai kashi 33.20 cikin 100 a watan Maris.
Hukumar ta bayyana hakan ne ta cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na X, hukumar ta ce hauhawar ta ƙaru ne daga kashi 31.7 cikin 100 na watan Fabarairu.
A cewar hukumar, wannan ya nuna hauhawar farashi ta ƙaru da kashi 11.16 cikin 100 a watan Maris ɗin 2024 idan aka kwatanta da yadda yake a watan Maris na 2023 da ya kasance kashi 22.04 cikin 100.
Kazalika ƙididdigar da NBS ta fitar ta nuna cewa hauhawar farashi a Maris ɗin 2024 ta kai kashi 3.02 cikin 100 saɓanin kashi 3.12 cikin 100 da aka gani a watan Fabarairu.
Read Also:
Hakan na nufin a watan Maris, ƙaruwar farashin kayayyaki ba ta kai wadda aka gani ba a watan Fabarairu.
Hauhawar farashi a watan Maris ta faru ne a lokacin da matakan da babban bankin Najeriya ke ɗauka na ɗaga darajar naira kan kuɗaɗen waje suka fara tasiri.
A makonnin baya-bayan nan darajar naira ta ƙaru a kan dala da fiye da kashi 40 cikin 100 daga kusan naira1,900 kan kowace dala zuwa kusan naira1,100 duk dala ɗaya.
Najeriya ta fuskanci hauhawar farashin da ba a taba gani ba a baya-bayan nan sakamakon faɗuwar darajar naira da kuma janye tallafin mai da gwamnati ta yi.
Sau biyu babban bankin ƙasar na ƙara kuɗin ruwa a bana a ƙoƙarin daidaita farashin kaya.
PRNigeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 21 hours 28 minutes 23 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 23 hours 9 minutes 48 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com