Asusun ba da lamuni na IMF ya amince da ƙunshin kuɗi na dala biliyan 3.4 ga Habasha bayan da gwamnati ta ƙyale kasuwa ta tantance darajar takardar kuɗin ƙasar.
A ranar Litinin ne, kuɗin ƙasar Birr ta rasa kusan kashi ɗaya bisa uku na darajarta a kan dala bayan matakan da gwamnati ta ɗauka.
Ƙunshin bashin na IMF zai taimaka wa Habasha a matakan garambawul ɗin da take ɗauka cikin shekara 4 masu zuwa.
Asusun zai gaggauta sakin kimanin dala biliyan ɗaya ga ƙasar da ke fama da ƙarancin kuɗaɗen waje da kuma hauhawar farashi a shekarun baya-bayan nan.
Habasha tana tattaunawa da hukumomin da ke bayar da bashi domin sake duba batun basussukanta.
Ƙasar ta daɗe tana neman tallafin sama da dala biliyan 10 daga IMF da bankin duniya.
PRNIgeria Hausa
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 11 hours 39 minutes 17 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 13 hours 20 minutes 42 seconds
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com