Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC ta ce gungun jami’an tsaro dauke da tarin makamai ya yi wa hedikwatarta da ke Abuja, dirar-mikiya.
Kungiyar ta ce jami’an sun isa ginin hedikwatar tata ne da ake kira Labour House, tun da daddare da misalin karfe 8:30
A sanarwar da shugaban sashen hulda da jama’a na kungiyar Benson Upah ya fitar ya ce jami’an sun karya kofar dakin da ke zaman ma’ajiyar littattafai da ke hawa na biyu na ginin inda suke debe daruruwan littattafai da wasu takardu
Read Also:
- Yusha’u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi Abdul
- Harin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309
- Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman Lafiya
Sanarwar ta ce, jami’an sun yi ikirarin cewa suna neman wasu takardu ne da aka yi amfani da su a zanga-zangar matsin rayuwa.
Kungiyar wadda ta ce zuwa yanzu ba ta iya tantance abubuwan da jami’an tsaron suka kwashe ba, ta nemi da a gaggauta janye jami’an daga hedikwatar tata.
Kungiyar ta bayyana yau a matsayin wata bakar rana a demukradiyyar Nijeriya, inda ta ce ko da a lokacin bakin mulkin sojoji ba a taba yi wa hedikwatarta abin da aka yi mata a wannan lokacin ba na kutse.
PRNigeria Hausa












