Home Labarai Ina sane da halin kuncin da kuke ciki – Tinubu

Ina sane da halin kuncin da kuke ciki – Tinubu

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya sake yin roƙo ga ƴan ƙasar su ƙara yi wa gwamnatinsa haƙuri inda ya ce sauƙi na nan tafe.

Shugaban ya sake yin jawabi ne ga ƴan Najeriya a wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na X ranar Laraba bayan jawabin farko da ya yi a ranar Lahadi saboda zanga-zangar tsadar rayuwa da kuma adawa da matakansa na tattalin arziki.

A cikin jawabin shugaban, ya nanata cewa yana sane da ƙuncin rayuwa da ƴan Najeriya suka shiga sakamakon janye tallafin fetur.

Ƴan Najeriya da dama ne suka fantsama a titunan biranen ƙasar domin zanga-zangar tsadar rayuwa, inda wasunsu da dama ke kira ga shugaban ya dawo da tallafin da ya cire na man fetur da suka ce ya jefa su cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa.

Amma a sabon jawabinsa, shugaban ya ce yana sane da wahalar da ƴan Najeriya ke ciki tare da nanata cewa wahala ce ta ɗan ƙaramin lokaci.

“Wannan lokacin zai iya zama mai wahala a gare mu amma ina son mu yi hangen gaba a cikin wahalar da muke ciki da kuma la’akari da babbar manufar. Mun yi tsare-tsare masu kyau kuma na san za su yi aiki,” in ji Shugaba Tinubu.

Sai dai shugaban ya amince cewa tsare-tsaren da gwamnatinsa ke ɗauka sun ƙara wa ƴan Najeriya raɗaɗin janye tallafin fetur.

Amma ya ce ya yi imanin matakan gwamnatinsa ke ɗauka za su magance matsalolin tattalin arzikin da Najeriya ke ciki.

“Ina roƙon ku, ku yi haƙuri tare da imanin cewa za mu iya da kuma damuwar da muke nunawa kan buƙatunku. Za mu fita daga cikin wannan ƙangin, kuma saboda matakan da muke ɗauka Najeriya za ta samu ci gaba da kuma more makomarta,” a cewar shugaba Tinubu.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Gwamnatin Tarayya ta Kaddamar da Kwamitin Bincike Kan Mutuwar Ma'aikatan Haƙar Ma'adinai 37 a Hukumar Kula da Haƙar Ma'adinai ta NSCDCMajalisar Dattawa ta 10 da Ma'anar Jagorancin Majalisa Daga Kabir AkintayoDarakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna Yusuf
X whatsapp