Home Labarai Jami’an tsaro sun kutsa Shalkwatar NLC

Jami’an tsaro sun kutsa Shalkwatar NLC

Kungiyar kwadago ta Najeriya ta NLC ta ce gungun jami’an tsaro dauke da tarin makamai ya yi wa hedikwatarta da ke Abuja, dirar-mikiya.

Kungiyar ta ce jami’an sun isa ginin hedikwatar tata ne da ake kira Labour House, tun da daddare da misalin karfe 8:30

A sanarwar da shugaban sashen hulda da jama’a na kungiyar Benson Upah ya fitar ya ce jami’an sun karya kofar dakin da ke zaman ma’ajiyar littattafai da ke hawa na biyu na ginin inda suke debe daruruwan littattafai da wasu takardu

Sanarwar ta ce, jami’an sun yi ikirarin cewa suna neman wasu takardu ne da aka yi amfani da su a zanga-zangar matsin rayuwa.

Kungiyar wadda ta ce zuwa yanzu ba ta iya tantance abubuwan da jami’an tsaron suka kwashe ba, ta nemi da a gaggauta janye jami’an daga hedikwatar tata.

Kungiyar ta bayyana yau a matsayin wata bakar rana a demukradiyyar Nijeriya, inda ta ce ko da a lokacin bakin mulkin sojoji ba a taba yi wa hedikwatarta abin da aka yi mata a wannan lokacin ba na kutse.

PRNigeria Hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba Hatsarin Jirgin Sama na Ondo: Disu Ya Jajantawa NAF, Ya Jaddada Goyon Bayan Ƴan SandaHukumar Kwastam ta Kwace Wiwi ta N3.67bn da Aka Boye a Cikin Motocin da Aka Shigo da su, da Sauran Kayayyaki a Tashar Jirgin Ruwa ta LegasFadada Rundunar Soja: COAS ya Yabawa Gwamnatin Nasarawa Kan Karbar Sabbin SojojiTaron Talla na Ƙasa 2026: Farfesa Sule Ya'u Sule zai yi Magana Kan Harshe, Al'adu da Talla a Arewacin NajeriyaSojoji Sun Yaye Kwamandoji na Musamman Domin Yaki da Ta'addanci da Jiragen Yaki Marasa MatukaMinista Ya Yaba da Aikin Babban Titin Tarayya na N1.5trn a Jihar NejaGwamnatin Tarayya ta Fito da Matakai 10 Don Rage Radadin Tsadar Man FeturKasuwar Hannun Jari ta Najeriya ta Rasa N1.34trnGwamnatin Tarayya ta Sanar da Rangwamen Man Fetur na Kwana 30 ta NNPC
X whatsapp