Jami’an tsaro a Najeriya sun kama ‘yan ƙasar Poland bakwai bisa zargin ɗaga tutocin Rasha yayin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihar Kano da ke arewacin ƙasar.
Kakakin rundunar tsaron farin kaya, Peter Afunanya, ya faɗa yayin taron manema labarai a yau Laraba cewa sun kama su ne lokacin da jami’ansu ke ƙoƙarin tabbatar da tsaro.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sai dai bai yi ƙarin bayani ba game da ko su wane ne, amma ba farautar ‘yan ƙasar ta Poland a Najeriya suke yi ba.
Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito jakadan Poland a Najeriya, Stanislaw Gulinski, yana tabbatar da kamen yayin ganawar da jakadu suka yi da gwamnatin Najeriya ranar Laraba a Abuja.
“An kama su kwana biyu da suka wuce a Kano, abu na ƙarshe da na ji shi ne ana shirin kawo su Abuja a jirgi,” in ji shi.
Sai dai ya ƙi yin ƙarin bayani lokacin da Reuters ya tuntuɓe shi.












