Rundunar sojin saman Najeriya ta ce sojojinta masu aiki ƙarƙashin shirin ‘Operation Hadin Kai’ da ke yaƙi da ayyukan masu tayar da ƙayar baya sun kashe manyan kwamandojin Boko Haram a hare-hare ta sama da suka kai a a ranar 16 ga wannan wata na Agusta a jihar Borno.
Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwar da rundunar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta AVM Edward Gabkwet a yau Laraba.
Sanarwar ta ce “rundunar ta kai harin ne kan ƴan ta’addan da suka yi hijira zuwa yankin daga wasu wurare da ke kusa”.
“Hare-haren sojojin ta sama sun yi nasarar halaka ƴan ta’adda da dama da suka hada da manyan kwamandojinsu biyar da kuma yaransu 35 tare da lalata maɓoyarsu da kayan aikinsu.
“Bayanai masu ƙarfi da aka tattara sun nuna cewa manyan ƴan ta’adda da ke a wurin da aka kai harin a daidai lokacin sun haɗa da Munzir Arika, Sani Dilla (Dan Hausawan Jubillaram), Ameer Modu, Dan Fulani Fari Fari, da Bakoura Arina Chiki, sai kuma sauran wasu ƴan bindiga 35.”
Sanarwar ta ce “Ana sa ran nasarar kashe waɗannan kwamandojin da mayakansu zai rage ƙarfin wadannan kungiyoyi ƴan ta’adda na ƙara kai hare-hare ko sake haɗuwa a yankin.”
Najeriya na yaƙi da mayaƙan ƙungiyar Boko Haram tsawon sama da shekaru 10 da suka gabata, rikicin da ya yi sanadin mutuwar dubban al’umma da kuma tarwatsa sama da mutum miliyan ɗaya daga gidajensu.
Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta yi iƙirarin karya lagon mayaƙan, amma har yanzu akan samu hare-hare nan da can a yankin na arewa maso gabashin ƙasar.
A ƙarshen watan Yuli, wasu mayaƙa da ake zargin ƴan Boko Haram ne sun kai hari a jihar ta Borno wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum 16.
Kidnapped School Children
Yauri FGC Students, Kebbi1254 days 19 hours 57 minutes 35 seconds,
Baptist School Students, Kaduna
1236 days 21 hours 39 minutes 0 second
Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Report By: PRNigeria.com