Shugaba Faye ya bayar da tabbacin zaɓen ‘yan majalisa bisa gaskiya da adalci

Shugaban kasar Senegal, Bassirou Diomaye Faye, ya ba da tabbacin a jiya Juma’a cewa, za a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki na ranar 17 ga watan Nuwamba, cikin ‘yanci da gaskiya, yana mai kira ga ‘yan siyasa da su kiyaye daga duk wani lamari da kan iya haifar da tashin hankali ko rudani.

Shugaban na Senegal ya na mai cewa “yayin da yakin neman zaben ‘yan majalisar dokoki ke gabatowa, ina gargadin dukkan ‘yan kasar Senegal, musamman ma ‘yan siyasa na ko wane bangare, da su guji wuce gona da iri a cikin maganganunsu da ayyukansu.”

Faye ya yi amfani da wannan dama tare da yin kira ga masu ruwa da tsaki da su kawo ta su goyon baya na ganin an cimma nasara a wannan zabe da sunan ceto kasar ta Senegal a karshe da kuma  tabbatar da cewa “zaben zai kasance cikin ‘yanci, dimokiradiyya da gaskiya”.

A ranar 17 ga watan Nuwamba ne ‘yan kasar Senegal za su zabi sabuwar majalisar dokoki, watanni takwas bayan zaben shugaban kasar da Diomaye Faye  ya yi nasara a zaben shugaban kasa da aka yi a zagayen farko da kashi 54% na kuri’un da aka kada. Za a fara yakin neman zaben a yau Asabar da dare.

Kidnapped School Children

Yauri FGC Students, Kebbi
1254 days 18 hours 41 minutes 27 seconds,

Baptist School Students, Kaduna
1236 days 20 hours 22 minutes 52 seconds

Tegina Islamiya Pupils, Niger (Freed)
Spent 88 days from May 30, 2021 - August 26, 2021


Report By: PRNigeria.com

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com