Home General Dalilin kotu na ɗage shari’ar Nnamdi Kanu har sai yadda hali ya...

Dalilin kotu na ɗage shari’ar Nnamdi Kanu har sai yadda hali ya yi

Babbar kotun tarayya da ke zama a Abuja, babban birnin Najeriya ta ɗage sauraron shari’ar da ake yi wa shugaban ƙungiyar masu rajin kafa ƙasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu.

Ana tuhumar Kanu da laifuka da dama, waɗanda suka jiɓanci ta’addanci, tun bayan kama shi da kuma mayar da shi Najeriya a watan Yunin 2021.

Tun a wancan lokacin ake ci gaba da tsare jagoran na IPOB, kuma duk wani yunƙuri na neman beli ya ci tura.

A baya an samu tsaiko wajen ci gaba da shari’ar bayan da Mista Kanu ya buƙaci mai sauraron ƙarar, Binta Nyako ta tsame kanta daga shari’ar kasancewar “ba ya da ƙwarin gwiwa a kan ta.”

Nyako ta sanar cewa ta tsame kanta daga shari’ar. To sai dai babban alƙalin kotun ya sake mayar wa alƙaliyar takardun shari’ar domin ta ci gaba da jan ragamarta, kasancewar Nnamdi Kanu bai gabatar da buƙatar tasa a rubuce ba.

A zaman na yau litini, mai shari’a Binta Nyako ta ce babban alƙalin kotun bai amince da janyewar tata ba.

Ta kuma buƙaci masu kare Kanu da su gabatar da buƙatarsu a rubuce, matuƙar suna nan a kan bakarsu ta cewa sai ta tsame kanta daga shari’ar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Dangote ya ƙara farashin man feturHukumar Jin dadin alhazan Kano ta sanar da ranar fara jigilar maniyatantaYadda Lakurawa suka kashe masallata a KebbiDSS ta kama jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo a EdoBa mu taɓa goyon bayan musguna wa Kristoci ba - Gwamnatin NajeriyaGobara ta tashi a babban kasuwar Fika da ke jihar YobeWaye Tunji Disu: Sabon Babban Sifeton 'Yansandan NajeriyaNijar ta amince da kundin ayyukan AES na shekara ta biyuAtiku ya zargi gwamnatin Tinubu da yi wa dimokuraɗiyya zagon ƙasaGwamnatin Kano ta fara tantance ’yan kasuwa da gobarar Singer ta shafa don rabon tallafiSojojin Nijeriya sun kashe Kwamandan Boko haram da mai sayar Musu da jirgin Drone a AdamawaHisbah ta kama mutum tara saboda rashin yin azumi a KanoMajalisar jihar Rivers ta dakatar da shirin tsige FubaraMasu haƙar ma’adinai 33 sun mutu sakamakon gubar sinadarin carbon a FilatoSojojin Amurka 100 sun fara aikin horar da Sojin Najeriya don yaƙi da ta'addanci
X whatsapp