Home Labarai Bani da lokacin yin cacar Baka da El’rufai- Ribado

Bani da lokacin yin cacar Baka da El’rufai- Ribado

Mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce ba shi da lokacin cacar baka da tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i wanda ya bayyana cewa Ribadu na haɗa kai da gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani da ICPC domin ɓata masa suna.

A ranar Litinin ne dai tsohon gwamnan na jihar Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i a tattaunawarsa da gidan talbijin na Arisetv ya yi zarge-zargen inda har ya ce Ribadu na yin duk abubuwan ne domin ya ɓata wa El-Rufa’i suna domin ya cika burinsa na takarar shugabancin Najeriya a 2031.

A shafinsa na Facebook, Nuhu Ribadu ya mayar da martani inda ya ce shi yanzu aikinsa ne a gabansa ba cacar baka da wani ba.

“An janyo hankalina kan wata tattaunawa da Mallam Nasir El-Rufa’i ya yi da yammacin Litinin. Ba don ka da ace shirun da zan yi ba alamar na amince da zarge-zargen nasa ne da na yi shiru. Ni yanzu ina da abin yi saboda haka ba ni da lokacin shiga kafar watsa labarai in yi cacar baka da El-Rufa’i ko ma wani daban.” In ji Ribaɗu.
Mai bai wa shugaban na Najeriya shawara kan tsaro ya ƙara da cewa ya kame daga faɗin abubuwa marasa daɗi ga tsohon gwamnan ne bisa la’akari da irin dangantakarsu.

“Duk da irin suka da yaƙa ta da El Rufa’i ke yi, ban taɓa faɗin wani abu mara kyau ba a kansa. Wannan kuma saboda irin yadda nake martaba alaƙarmu da shi ta baya da irin abotar da ke tsakanin iyalanmu. Saboda haka abin da ban yi a baya ba yanzu ba zan fara ba. Amma dai ina kira ga al’umma da su yi watsi da zarge-zargen El Rufa’i a kaina.”

Dangane kuma da takarar shugabancin Najeriya a 2031 da El-Rufa’in ya yi zargi, Malam Nuhu Ribadu ya ce:

“Domin gujewa duk wani zato, zan faɗi cewa ban taɓa tattauna takarar neman shugabancin ƙasar nan a 2031 da wani ba. Na mayar da hankalina da tunanina kan yadda za a ciyar da Najeriya gaba da kuma nasarar shugaba Bola Ahmed Tinubu.” In ji sanarwar.

Daga ƙarshe Mallam Nuhu Ribaɗu ya nemi El-Rufa’i da ya saurara masa domin ya samu damar mayar da hankali wajen aikin da ke gabansa “kamar yadda ban damu da al’amuransa ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp