Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya amince da nadin Birgediya Janar Kunle Nafiu matsayin sabon babban daraktan Hukumar yiwa kasa hidima ta NYSC.
Kafin nadin shine shugaban ma’aikatan Ofishin babban hafsan hafsoshin kasar Laftanar Janar Olufemi Oluyede, haka ya rike irin wannan mataki lokacin tsohon hafsan hafsoshin Marigayi Laftanar Janar Abiodun Lagbaja.
Read Also:
Birgediya Janar Nafiu guda ne cikin sojojin da suka fito daga cikin wadanda aka yaye a rukunin (47 regular Course) bangaren sojojin Atilare daga Kwalejin manyan sojoji ta Nijeriya da kuma Kwalejin yaki ta Amurka.
kafin zamansa shugaban ma’aikatan Ofishin babban hafsan hafsoshin kasar, ya rike mukamin daraktan ma’aikata na kwalejin yaki ta Nijeriya,
sabon babban daraktan hukumar ta NYSC ya fito daga garin Ileogbo, dake karamar hukumar Aiyedire a jihar Osun.
Nadin na Birgediya Janar Kunle Nafiu zai fara aiki nan take, wanda zai maye gurbin tsohon daraktan hukumar Birgediya Janar Yushau Ahmed.










