Home General NLC ta Gargadi NERC kan yunkurin kara kudin wutar lantarki a Nijeriya

NLC ta Gargadi NERC kan yunkurin kara kudin wutar lantarki a Nijeriya

Ƙungiyar kwadago ta Najeriya, NLC, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dakatar da yunƙurin ƙara kuɗin lantarki da masu amfani da layin A da B da C.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar lahadi, bayan wani taro da ta yi a jihar Adamawa dake arewa maso gabashin Nijeriya, inda ta bayyana rashin amincewar ta ta yunkurin na kara farashin wutar a kasar

“NLC ba ta amince da yunƙurin hukumar lantarki ta Najeriya NERC na ƙoƙarin sauya layin lantarki kwastomomi daga layin B da A da sunan haɓaka samun lantarki, alhali kuma yunƙuri ne kawai na ƙara wa mutane kuɗin wuta ba tare da sun shirya ba,” in ji sanarwar.

“A fili yake dai yanzu masu ƙarfi a ƙasar na ƙara jefa marasa ƙarfi cikin ƙunci ta hanyar ƙara kuɗin haraji da lantarki da sauransu a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ya tsaya cak.”

Ƙungiyar ta ƙara da cewa ba za ta lamunci ƙarin kuɗin wutar ba, inda ta yi barazanar shirya zanga-zanga idan har aka ƙara kuɗin lantarkin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp