Wasu bayana na bayyana cewa a kalla Mayaƙan al Shabab fiye da 40 ne suka mutu a wani gumurzu tsakaninsu da dakarun Sojin Somalia a ƙarshen mako, dakarun gwamnatin dai na ci gaba da samun galabar mafi girma a baya-bayan nan.
Sanarwar da rundunar Sojin Somalia ta wallafa a shafinta na X aka kuma sanar a gidan talabijin mallakin gwamnati a daren Lahadi, ta ce dakarunta sun hallaka mayaƙan fiye da 40 a yankin Hirshabelle.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sanarwar ta ci gaba da cewa, dakarun Sojin sun ƙaddamar da hare-haren da taimakon dakarun ƙasashe da ke taimaka musu a yaƙi da al Shabaab ta yadda suka yi musu ƙawanya a maɓoyarsu da ke Biya Cadde a yankin na Hirshabelle.
Rundunar Sojin ta Somalia ta ce har zuwa yanzu dakarun na ci gaba da luguden wuta a maɓoyar mayaƙan na al Shabaab.
A baya-bayan nan Sojojin Somalia na samun nasara kan mayaƙan al Shabaab inda ko a watan jiya ta hallaka da dama daga cikinsu kwanaki bayan Amurka ta musu luguden wuta da jiragen yaƙi.












