Home General Matatar Ɗangote za ta maida wa kwastomominta naira 65 kan kowace lita...

Matatar Ɗangote za ta maida wa kwastomominta naira 65 kan kowace lita man fetir

Matatar Dangote

Wanan mataki dai ya biyo bayan sanarwar da kamfanin ya yi na rage farashin litar man fetur, inda ya ce za a rinƙa siyar da ita kan naira 825 saɓanin naira 890.

A cikin wata sanarwa da matatar ta fitar a ƙarshen mako, ta tabbatar da cewar za ta maida wa duk wani ɗan kasuwar naira 65 kan kowa ce lita da ya siya, a cikin sama da tan dubu ɗari 2 da aka saida wa ƴan kasuwa, kan Naira 890 bayan sanar da sabon farashin na Naira 825.

Matatar ta Ɗangote ta buƙaci waɗanda suka siya litar man fetur sama da naira 825 bayan sanarwar rage farashin, a hannun abokan hulɗarta AP da Heyden da kuma MRS a duk faɗin Najeriya, su kai wa kamfanin risitinsu don maida musu da kuɗin da aka ƙara musu, wanda hakan ya sa matatar ta Ɗangote, za ta yi asarar Naira biliyan 16, a ƙoƙarinta na sauƙaƙa wa ƴan Najeriya.

Wannan matakin, da ya fara aiki a ranar 27 ga Fabrairu 2025, ya tabbatar da cewa babu wani abokin kasuwancinmu da zai yi asara saboda rage farashin da muka yi. Abu mai mahimmanci kuma shi ne, ragin farashin man fetur ɗin ya fara aiki nan take, don amfanin al’ummar Najeriya.

Matatar ta Dangote ta kuma yi ala wadai da duk wani mataki da wani zai ɗauka don daƙile walwalar ƴan Najeriya, ta hanyar sai da makamashin sama da naira 825 kan kowa ce lita.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp