Home General BINCIKE: shin da gaske ne hukuma ICPC ta kai sumame Ofishin NAHCON...

BINCIKE: shin da gaske ne hukuma ICPC ta kai sumame Ofishin NAHCON saboda tallafin aikin Hajji

An wallafa wasu rahotannin a jaridun kasa da ke ikirari cewa jami’an hukumar dake haki da cin hanci da rashawa ta ICPC sun yiwa hukumar Alhazai ta NAHCON da ke Abuja dirar mikiya a ranar laraba bisa karkatar da kudin tallafin aikin hajjin shekarar 2024 da ya kai Naira biliya 90.

Rahotannin ya ce dakarun hukumar ta ICPC sun yi dirar mikiya a ofishin hukumar ta NAHCON, abin da ya sa aka dakatar da dukkannin ayyukan da ake ofishin.

Da ya ke kokarin tabbatar da sahihancin labarin sashen binciken sahihancin labara na PRNigeria  ya tuntubi kakakin hukumar ta NAHCON Fatima Sanda Usara, wadda ta ce jami’an hukumar ICPC ba su yi dirar mikiya a hukumar ba.

“ba dirar mikiya suka yi ba, kawai sun zo ofishin mu ne domin ganin manyan mu, wadanda suka gayyata a baya saboda ‘yar matsalar dake faruwa a hukumar, su wadanda jami’an suka zo nema basa nan ma lokacin basu ma shigo Ofis ba. Sun jira a waje, lokacin da ya zo kuma sun gana sannan kuma su ka tafi salin-alin. Zuwan nasu bashi da alaka da shugaban hukumar kamar yadda jaridar Guardian ta wallafa,” kamar yadda ta bayyana.

Domin tabbatar da kalaman na ta sashen binciken na PRNigeria ya tuntunbi mai Magana da yawun hukumar ta ICPC, Demola Bakare wanda ya tabbatar da kalaman na Usara da cewa sun kai ziyarar aiki ne kawai.

“E, mun binciki jami’in hukumar NAHCON. Saboda bai amsa gayyatar da muka yi masa ba. Wannan ne ya sa muka kai masa ziyara. Ba mu rufe hukumar ba kamar yadda wasu suka bayyana. ICPC na gudanar da ayyukanta ne bisa tanadin doka.

“Mun kama jami’in, wanda bazan fada maka sunan sa ba, tuni kuma mun bayar da shi kan beli wanda daga yanzu kuma zai cigaba da taimakawa hukumarwajen gudanar da bincike,” kamar yadda Bakare ya bayyanawa PRNigeria.

Akwai dai wani labara, da PRNigeria ta samu da ke cewa akwai wani bincike na naira billiya 90 na tallafin hajji da aka mikawa hukumar dake yaki da masu yiwa tattalin arziki ta EFCC ba hukumar ICPC ba.

A ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2023, jaridar Punch ta ruwato cewa hukumar EFCC ta gayyaci shugaban hukumar NAHCON, Alhaji Jalal Arabi domin ya yi mata bayani kan yadda hukumar ta kasha kudin tallafin aikin hajjin na naira biliyan 90 a shekarar 2024.

Arabi tun da fari ya yi bayanin cewa naira biliyan 90 da shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya Amince da ita an yi amfani da ita ne wajen tallafin aikin hajjin da kuma wasu ‘yan kunji-kunji.

An ambace shi yana cewa, “an tallafawa ko wannen maniyyaci da N1,637,369.87 da ga cikin naira biliyan 90 banda alhazan da suke karkashin tsarin ajiya na hukumar hajji wadanda sun sami abin da ya fi haka.

KAMMALAWA: binciken da Jaridar PRNigeria ta gudanar ya tabbara da cewa hukumar ICPC ba ta yiwa hukumar NAHCON dirar mikiya ba, bata kuma rufe ofishin hukumar ba kamar yadda yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito. Hukumar dake yaki da cin hancin ta kai ziyarar aiki ne hukumar bisa wani bincike.

PRNigeria ta yanke hukunci cewa ikirarin da aka yin a cewa hukumar ICPC ta yi dirar  mikiya hukumar NAHCON saboda zargin batan kudin tallafin aikin hajji naira biliyan 90 ba gaskiya bane Karya ne.

PRNigeria

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Mayaƙan Lakurawa Sun Kashe Sojoji 7 a SokotoAn faɗa wa Shugaba Tinubu Cewa Ina Kitsa Yadda Zan Kashe Shi - ShettimaRundunar 'Yan Sandan Najeriya ta Ceto ƴan Mali 30 Daga Hannun Masu Safarar MutaneMun Kashe Mayaƙan ISIS 175 - Rundunar Sojin NajeriyaFarfesa Pantami ya Janye Daga Takarar Gwamnan Jihar GombeKishiya: Tsakanin ONSA na Ribadu da Tsaron Gida Famadewa Daga Yushau A. ShuaibZaben Fidda Gwani: An Harbe Mutum a Jihar PlateauRundunar 'Yan Sanda ta Tabbatar Kashe Jami'anta 17 a YobeSatar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe'Yan Bindiga Sun Sace Basarake Tare da Mata 2 a KatsinaJami'an Kwastam Biyu sun Rasa Ransu a Fafatawa da LakurawaMatar Aure ta Zuba wa Kishiyarta da 'Ya'yanta Biyu Fetur Tare da Banka Musu Wuta a KanoIna da ƴancin Mu'amala da Kowa ba Tare da La'akari da Jam'iyya ba - WikeAdadin Masu Fama da Cutar Tamowa na ƙaruwa a Najeriya - MSFGwamnatin Yobe ta Sha Alwashin Kawo ƙarshen Hare-Haren Boko Haram
X whatsapp