Allah ya yiwa shahararren malamin addinin musuluncin nan Sheikh Khalifa Usman kusfa Zaria Wanda aka fi Sani da Rigi-rigi rasuwa.
Sirikinsa Abubakar Ɗanyaro ne ya bayyana hakan a daren Lahadi a jihar Kaduna, wanda ya ce ya rasu a asibiti bayan gajeriyar jinya.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sheik Khalifa Usman guda ne cikin malaman addinin musulunci da yayi shuhura a kafafen sada zumunta.
Ana sa ran za a yi masa sallar jana’iza a gidansa da ke Zariya a yau Litinin, bayan sallar La’asar .
A yan shekarun nan, malamin ya shahara a shafukan sada zumunta bisa salonshi na wa’azi
Fatanmu Allah Ya gafarta masa da sauran Musulmi baki ɗaya.












