Akalla shaguna 25 da Katina 19 ne a ka tabbatar sun kone a babbar Kasuwar Singa da ke a birnin Kano a arewacin tarayyar Najeriya.
Mai magana da yawun hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi ne ya tabbatar da haka a wata rubutacciyar sanarwa.
Hukumomi a Kano dai sun bayyana cewar gobarar da haddasa hasarar kaya na miliyoyin Naira kamin daga bisani a ka samu nasarar kashe Wutar.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wutar ta tashi ne da misalin karfe 5 na Asubah kuma daga nan ne mutane su ka nemi agajin gaggawa daga hukumar kashe gobara ta jihar abin da ya takaita matsalar da kuma kare akalla shaguna 24 daga konewa.
Matsalolin hanya da ke da nasaba da manyanyan Motocin dakon kaya da ake ajiyewa a wurin cikin kasuwar na daga cikin matsalolin da su ka ta’azzara matsalar.
Wutar ta samo asali ne daga wayoyin Wutar lantarki a daya daga cikin shagunan da su ka kone, saidai ba a samu rasa rayka ba.












