Home Labarai Satar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe

Satar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe

Arrest

Satar Kayayyakin Banki: An Kama Mutane Huɗu a Jihar Gombe

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Gombe ta kama wasu mutum huɗu da ake zargi da hannu wajen satar kayayyaki a Bankin Bayar da Lamunin Gidaje na Tarayya da ke birnin Gombe.

Wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, DSP Buhari Abdullahi, ya raba wa manema labarai a Gombe ta ce ana ci gaba da neman wani daga cikin ababen zargin da ya tsere.

Sanarwar ta bayyana sunayen waɗanda aka kama dukkaninsu matasa da suka fito daga unguwanni daban-daban da ke jihar.

Kakakin ’yan sandan ya ce wani ma’aikacin bankin ne ya shigar da ƙorafi kan lamarin a ranar 15 ga Mayun 2026.

Ma’aikacin bankin ya zargi ɗaya cikin matasan, Umar Sa’idu da haɗa baki da wani mutum mai suna “Rasha”, wanda ya tsere, wajen shiga bankin da ke yankin GRA inda suka yi awon gaba da kayayyakin.

Kayayyakin da aka ce an sace sun haɗa da batir ɗin solar guda huɗu, kwamfutar tafi-da-gidanka nau’in HP, na’urar CCTV decoder da kuma wayar Nokia mai madannai.

Bayan samun rahoton, jami’an ’yan sanda na sashen Pantami suka fara bincike, wanda ya kai ga cafke waɗanda ake zargin tare da kwato wasu daga cikin kayan da aka sace.

A binciken da aka gudanar, an gano batirin solar guda huɗu, kwamfutar HP da kuma na’urar CCTV decoder, yayin da ake ci gaba da neman wanda ya tsere da kuma sauran kayan da aka nema aka rasa.

A wani labarin makamancin wannan, rundunar ta kuma kama wani mutum mai suna Muhammad Bello, mai shekaru 35 daga unguwar Bolari, bisa zargin yunƙurin fashi da makami a yankin Nee GRA da ke kusa da makarantar Pen Resource a Gombe.

’Yan sanda sun ce an kama shi ne bayan samun kiran gaggawa, inda jami’an ofishin Pantami suka kai ɗauki cikin hanzari.

An kuma gano guduma da ake zargin an yi amfani da ita wajen kai harin tare da wani babur nau’in Boxer a hannunsa.

Mutumin da harin ya rutsa da shi ya samu raunuka, inda aka kai shi asibiti domin kula da lafiyarsa kafin daga bisani aka sallame shi.

Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, CP Umar Ahmed Chuso, ya sake jaddada ƙudirin rundunar wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’a a faɗin jihar.

Ya kuma buƙaci al’umma da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro sahihan bayanai cikin lokaci domin taimaka wa yaƙi da laifuka da inganta tsaro.

Rundunar ta ce yanzu haka bincike na ci gaba da gudana kuma da zarar ta kammala za a gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa'adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDPAIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da ZamfaraSojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta'addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a SokotoCOAS Shaibu ya yi Kira da a Haɗa Kai Yayin da Sojoji Ke Faɗaɗa Zuwa Rukunoni 12Najeriya ta Shirya Horarwa ta Yankuna Kan Gano da Bin Diddigin Ƙananan MakamaiSojoji Sun Kai Harin Sama da ya Hallaka Ƴan ISWAP Sama da 40, ya Lalata Motoci a BornoAmurka ta Zargi Najeriya da Daukar Yara Sojoji, Masana'antun Jarirai da Fataucin MutaneHaɗaka DMI da TMS a London ta Tsara Sabuwar Hanyar Goyon Bayan Tinubu Zuwa 2027Yushau Shuaib @57: Bikin Jagora Wanda ya Buɗe Kofofi da Canza Rayuka Daga Hafsat Ibrahim Yusha'u Shuaib @57: Barka da zagayowar Ranar Haihuwa ga Jagoran Mazaje, Mutumin da Ya Bani Dama Daga Ozumi AbdulHarin Jirgin Sama a Filin Jirgin Saudiyya ya yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane 12, Raunata 309Trump ya yi Kira ga Sabon Shugaban Ukraine, ya Zargi Zelensky da Kin Amincewa da Yarjejeniyar Zaman LafiyaAFRI-CIRD ta yi Kira ga Gwamnatoci su Kara Kudin Ilimin Ƴa'ya MataAmnesty International ta yi Allah Wadai da Toshe Taron 'Dole Tinubu Ya Tafi' da Ƴan Sanda Suka yi a KanoTMG vs TMS: Matsalar Sadarwa Kan Makomar Tinubu Daga Yushau A. Shuiba 
X whatsapp