Jerin Sunayen Kayayyakin da Gwamnatin Rasha ta Hana a Shigar da su ƙasarta
Gwamnatin Rasha ta sanar da jerin kayayyaki fiye da 200 da ta hana shiga da su ƙasar daga ƙasashen waje.
Kayayyakin sun ƙunshi na sadarwa da harkokin lafiya, da ababen hawa, da injinan noma, da na lantarki, da ƙarafen layin dogo, da injinan sarrafa duwatsu, da majigi da sauransu.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Wata sanarwa daga fadar gwamnatin ta ce da ma an dakatar da shigar da kayan na ɗan wani lokaci amma yanzu haramcin zai ci gaba har zuwa ƙarshen 2022.
“Wannan matakin ya zama dole don tabbatar da samun natsuwa a kasuwannin Rasha,” a cewar sanarwar.
Matakin na zuwa ne yayin da ƙasashe da kamfanonin duniya ke ci gaba da ƙaurace wa harkoki da Rasha da zimmar matsa mata ta janye dakarunta da ke luguden wuta a Ukraine tun daga ranar 24 ga watan Fabarairu.












