Home Labarai DHQ zata bada Miliyan Biyar ga wanda ke da bayani kan yadda...

DHQ zata bada Miliyan Biyar ga wanda ke da bayani kan yadda za’a cafke ‘yan ta’adda

Shalkwatan Tsaron Najeriya ya wallafa sunaye tare da hotunan wasu kwamandojin ‘yan ta’addar da suka addabi arewa maso gabashi da kuma arewa maso yammaci da tsakiyar arewacin Najeriya.

Shalkawatan tsaron ta ce, zata bada tukuicin Naira miliyan 5 ga duk wani dan Najeriya da ke da bayanai kan yadda za a iya cafke ‘yan ta’addar.

wannan dai na wani bangare na daukar matakin ci gaba da aikin kakkabe mayakan dake tayar da kayar baya a yankunan. abin da ta bayyana mayin aikin daya rataya a wuyan ta maido da da zaman lafiya a yankunan.

Sunayen ‘yan ta’addar da ake nema ruwa a jallo kamar yadda darektan yada labaran shalkwatan tsaron Manjo Janar Jimmy Akpor ya fitar, sun hadar da:

SANI DANGOTE – daga kauyen  Dumbarum, Karamar Hukumar Zurmi ta jihar Zamfara.

BELLO TURJI GUDDA – daga kauyen Dakai, jihar Zamfara.

LEKO – daga kauyen Mozol, jihar Katsina.

DOGO NAHALI – daga kauyen ‘yar tsamiya, Karamar Hukumar  Kankara, jihar Katsina.

HALILU SUBUBU – daga kauyen Sububu a Karamar Hukumar Maradun, jihar Zamfara.

NAGONA –  daga Angwan Galadima da ke ISA a jihar S|okoto.

NASANDA – daga kauyen Kwashabawa, Karamar Hukumar Zurmi, jihar Zamfara.

ISIYA KWASHEN GARWA – daga kauyen Kamfanin Daudawa da ke Faskari a jihar Katsina.

ALI KACHALLA da aka fi sani da  ALI KAWAJE – daga kauyen Kuyambara a jihar Zamfara.

ABU RADDE – daga kauyen Varanda a Karamar Hukumar Batsari, jihar Katsina.

DAN-DA – daga kauyen Varanda a Karamar Hukumar Batsari, jihar Katsina.

SANI GURGU – daga kauyen Varanda a Karamar Hukumar Batsari, jihar Katsina.

UMARU DAN NIGERIA – daga kauyen Rafi da ke Mada a Gusau, jihar Zamfara.

NAGALA – daga Maru a jihar Zamfara.

ALHAJI ADO ALIERO – daga kauyen Yankuzo, a Karamar Hukumar Tsafe, jiharZamfara.

MONORE – daga ‘Yantumaki, jihar Katsina.

GWASKA DANKARAMI – daga kauyen Shamushele a Karamar Hukumar Zuri, jihar Zamfara.

BALERI – daga Karamr Hukumar Shinkafi, jihar Zamfara.

MAMUDU TAINANGE – daga kauyen baranda, Karamar Hukumar Batsari, jihar Katsina.

daga bisani shalkwatar ta ce ga dukkan mai wani karin bayani kan wadannan ‘yan ta’adda sai ya kira 09135904467 domin yin bayani.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
HOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da WiwiZakari Mohammed: Dole Kwara ta Cika Kwarewarta – Dan Takarar ADC ya Nemi Muhawara a BayyaneWSCIJ ta Yaba wa PRNigeria Kan Ci Gaba da Tallafawa Matasa Wajen Sadarwa Bayan Karewar Tallafi
X whatsapp