Khalifan Tijjaniyya, Muhammadu Sanusi II ya yi gargaɗi cewa Najeriya ta fi fama da rarrabuwar kai saboda ƙabilanci da bambancin addini tun bayan yaƙin Biafra fiye da shekara 50 da ta wuce.
Da yake jawabi a wani taro a Legas, Muhammadu Sanusi wanda ya ce “ba na tunanin Najeriya ta taɓa kasancewa a mawuyacin yanayi kamar yanzu tun bayan yaƙin basasa. Muna da ƙalubale game da aikin gina ƙasar nan.
Ya ce Najeriya tana fama da bambance-bambancen addini da na ƙabilanci.
“Muna da tattalin arzikin da ke fuskantar taɓarɓarewa kuma abin takaici, da alama muna fama da ƙarancin shugabanci na gari.”
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Kalaman tsohon gwamnan CBN ɗin na zuwa ne yayin da Shugaba Muhammadu Buhari ke shirye-shiryen miƙa mulki ga Bola Tinubu.
Tinubu ne ya yi nasara a kan manyan abokan takararsa – Atiku Abubakar da Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasar mai zafi da aka yi a watan Fabrairu.
Atiku da Obi sun yi fatali da sakamakon zaɓen, kuma tuni suka shigar da ƙara a kotu












