Majalisar wakilai ta Najeriya ta tsoma baki cikin batun zargin da hukumar shirya jarabawar shiga jami’a (JAMB) ta yi wa wata daliba mai suna Mmesoma Ejikeme na kirkirar sakamakon jarabawa na bogi wanda hukumar ta shirya na shekarar 2023.
‘Yan majalisar sun nuna damuwarsu kan yadda hukumar jarabawar ta gaza nuna dattaku kan lamarin da ya shafi karamar yarinya ta hanyar janye sakamakon jarabawarta tare da dakatar da ita na tsawon shekaru uku.
Read Also:
- An Cire Pantami: Lauyoyi 5 Sun Bai wa INEC Wa’adin 14 ga Oktoba Don Wallafa Sunan Ɗan Takarar PDP
- AIG Ahmed Musa ya Karbi Aiki a Matsayin Shugaban Ƴan Sanda na 25 na Yankin 10, ya yi Alkawarin Inganta Tsaro a Sakoto Kebbi da Zamfara
- Sojoji Sun Kashe Wanda Ake Zargi da Aikata Ta’addanci, Sun Kwato Bindigar AK-47 a Sokoto
Sun ce yana yiwuwa akwai hannun wani a cikin lamarin.
Daga nan ne majalisar ta kafa kwamitin da zai binciki lamarin tare da neman hukumar JAMB da ta dakatar da zartar da hukunci har sai majalisar ta kammala bincikenta.
A ranar Lahadin da ta gabata ne hukumar ta JAMB ta zargi dalibar da kirkirar sakamakon bogi a jarabawar ta bana.
PRNigeria hausa












