Home Labarai Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 22 a Katsina

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 22 a Katsina

Rundunar sojin sama ta Najeriya ta hallaka akalla ‘yan bindiga 22 a ƙananan hukumomin Jibiya da Batsari a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar.

PRNigeria ta ruwaito ce wa ‘yan bindigar – waɗanda galibinsu yaran riƙaƙƙen ɗan bindigar nan ne da aka hallaka Abdulkareem Boss – an kashe su ranar Litinin, a wani hari ta sama da dakarun rundunar ‘Hadarin Daji’ mai yaki da ‘yan bindiga – a yankin arewa maso yammacin ƙasar – ta kai.

Wata majiya mai ƙarfi a rundunar sojin ta shaida wa PRNigeria cewa an kai harin ne a kan tsaunukan da ‘yan bindigar ke ɓoye, bayan samun bayanan sirri da ke nuna cewa suna kitsa wani hari domin yin garkuwa da matafiya a kan hanyar Jibiya zuwa Katsina.

Majiyar ta ce ‘yan bindigar sun addabi al’umomin yankin, inda suke yin garkuwa da mazaunan wasu yankuna a ƙaramar hukumar Kankara.

Harin wanda ya yi sanadin mutuwar ‘yan bindiga da dama, ya kuma lalata sansanonin ‘yan bindigar.

A cikin watan Agustan 2022 ne dai rundunar sojin sama ta Najeriya ta kashe fitaccen ɗan bindigar nan mai suna Abdulkareem Boss tare da wasu daga cikin yaransa a wani hari ta sama da rundunar ta ƙaddamar kan maɓoyarsu a dajin Ruga da ke jihar Katsina.

An zargi Abdulkareem da kitsa wani mummunan hari da ya yi sanadin kashe wani babban baturen ‘yan sanda a ƙaramar hukumar Dutsinma ranar 5 ga watan Yulin 2022.

Mai magana da yawun rundunar sojin sama ta Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet, wanda ya tabbatar da harin na ranar Litinin, ya ce babban hafsan sojin sama na ƙasar, Air Vice Marshal Hasan Abubakar, ya umarci dakarun sojin saman ƙasar da su haɗa kai da sauran jami’an tsaro domin kakkafe duka ‘yan ta’addan da kuma maɓoyarsu.

PRNigeria hausa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com
Latest News
Darakta Janar na NITDA ya yi Kira da a Hada Hannu Kan Tsarin AI a Taron Manyan ShugabanniƳancin Sanin Gaskiya: Bayani Game da Tsarin Gudanar da Harkokin Sadarwa na Najeriya Daga Franklyn Ginger-EkeHOTO: NSCDC ta Tsare Jami'ai 24 Kan Mutuwar Masu Hakar Ma'adinai a TsareShirin Tallafin Mai: Atiku ya yi Watsi da Gaskiyar Magana – APCGwamnatin Tarayya ta Inganta Samar da Abinci ta Hanyar Shirin AgriShield na ONSA Daga Chido OnumahAtiku ya yi Tambaya Kan Rashin Zuwa UNGA a Karo na Uku da Tinubu ya yi, ya Nemi Karin BayaniFalconets ta Fice Daga Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata Ƴan Kasa da Shekaru 20 Bayan Colombia ta Sha Kashi a Wasan KarsheMatawalle Ya Nemi Tallafin Czech Don Samar da Alburusan DICON da Canja FasahaRundunar Sojojin Najeriya Ta Tallafa wa Iyalan Sojojin Gambia da Suka MutuFilato: Sojoji Sun Kama Masu Garkuwa 11, Sun Kwato MakamaiOPHK ta yi Bayani Kan Rahoton Amnesty na 2016 Dangane da Mutuwar da Ake Zargi a Barkin Giwa2027: Sama da Mambobin Jam'iyyar NDC 6,000 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP a EnuguKwankwaso ya Nuna Aniyar Yin Sulhu da Gwamna YusufYadda Hon. Hudu Kanje Ya Sake Fasalin Jagorancin Cigaban Kasa Daga Mika'il Ja'afarƳan Sanda Sun Kama Mutane 300 a Farmakin Wuraren da Ake Aikata Laifuka a FCT Sun Kwace Wukake, Bindigar Wasa, da Wiwi
X whatsapp